✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An zargi wadanda suka halarci taron ‘rantsar’ da Odinga da cin amanar kasa

‘Yan siyasa a kasar Kenya da suka halarci taron ‘rantsar’ da shugaban hamayyar kasar, Raila Odinga sun shiga cikin layin wadanda ake zargi da cin…

‘Yan siyasa a kasar Kenya da suka halarci taron ‘rantsar’ da shugaban hamayyar kasar, Raila Odinga sun shiga cikin layin wadanda ake zargi da cin amanar kasa.

Daga cikin wadanda ake zargi da cin amanar kasar akwai ‘yan majalisa guda biyu, wadanda suka halarci taron duk da cewa an sake su bayan ‘yan sandan kasar sun kama su da farko.

Bayan dai zaben da Shugaba Uhuru Kenyata ya sake samun nasarar lashe wa, da yawa daga cikin magoya bayans Raila Odinag sun gudanar da wani zanga-zangar a Gabashin kasar, inda a nan ne Odinga din ke da masoya da yawa domin a cewarsu, ai shi ne ya lashe zaben ba Uhuru Kenyata ba.

Haka kuma an kama lauya Miguna Miguna, sannan kuma aka far wa gidansa duk da cewa daga baya an bayar da belinsa a kan kudin Kenya dubu 50 wanda ya yi daidai da Dala 500, amma ya ci gaba da zama a komar ‘Yan Sanda har zuwa ranar da aka gabatar da shi a gaban shari’a domin sauraron kara a kotun Kajiado da ke mawabtaka da birnin Nairobi.

A kotun an gabatar da cewa ana kararsa ne bisa zarginsa da ake yi da cin amanar kasa, amma Miguna ya ki bayar da jawabi, inda ya ce lallai sai an mayar da shara’ar kotu a Nairobi.

Sai dai duk da cewa an kama yawancin wadanda suka halarci taron ‘rantsarwar’ da ‘yan hamayyar suka shirye, har yanzu ba a kama mai gayya mai aikin ba wato shi shugaban na su Raila Odinga.

Tuni magoya bayan Odinga suka fara zanga-zangar a kan zargin da ake yi wasu daga wadanda suka halarci taron, inda suka mamaye tituna har ma suka yi arangama da ‘yan sanda a Gabashin birnin Kisumu, sannan ‘yan sandan suka rika jefa musu barkonan tsuhuwa domin tarwatsa su, kamar yadda wani ya shaida wa Reuters.

Idan ba a manta ba dai, Odinga ya ‘rantsar’ da kan shi a matsayin Shugaban kasar Kenya ne ‘yan kwanakin da suka wuce bayan nuna rashin amincewa da shi da magoya bayansa suka yi da sakamakon zaben da Uhuru Kenyata ya sake lashe we.