An zargi wani ma’aikacin lafiya mai shekara 42 da yi wa wani yaro dan shekara 12 fyade a Abuja.
Hukumar Yaki da Safarar Mutane ta Kasa (NAPTIP) ce ta tabbatar da cewa ta kama mutumin.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito wata sanarwa da jami’a mai kula da Sashen Hulda da Jama’a a hukumar ta NAPTIP Stella Nezam ta fitar ranar Alhamis tana cewa an aikata laifin ne ranar Asabar 21 ga watan Maris.
“Yaron ya taso ne daga makarantar Islamiyya da rana, sai ya biya ta gidan su abokinsa da ke makwabtaka da wanda ake zargi.
“Da ya je ya yi ta kwankwasa kofa ba a amsa ba; ya juya zai tafi sai wanda ake zargin ya kira shi.
“Da yaron ya je sai ya fisgo hannunshi ya shige da shi falonsa inda ya yi lalata da shi”, inji sanarwar.
Hukumar ta NAPTIP ta ce wannan laifi ya saba da Dokar Haramta Cin Zarafi ta shekarar 2015.
Ta kuma ce tana ci gaba da bincike a kan lamarin.