✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An zargi Kwamandan Hisbah da karkatar da kayan tallafin COVID19 a Kano

Jami'an Hukumar Hisbah a Karamar Hukumar Dala dake jihar Kano sun zargi Kwamandan hukumar a yankin da karkatar da kayan tallafin COVID-19

Jami’an Hukumar Hisbah a Karamar Hukumar Dala dake jihar Kano sun zargi Kwamandan hukumar a yankin, Malam Suyudi Muhammad Hassan da karkatar da kayan tallafin COVID-19 da Karamar Hukumar Dala ta ba su don rage radadin da zaman kullen annobar ya haifar.

A cikin wata takardar korafi da jami’an su kimanin 73 suka aike wa Hedikwatar Hukumar Hisbah ta jiha, sun bukaci Babban Kwamadan hukumar, Ustaz Harun Ibn Sina da ya bincika lamarin.

Takardar korafin ta bayyana cewa kayayyakin da ake zargin kwamadan da karkatar da su sun hada  da buhun shinkafa 50 da katan taliya 50 da taliyar yan yara ita ma katan 50.

A cewar jamian, tun daga lokacin da Karamar Hukumar ta bayar da kayayyakin aka neme su sama ko kasa aka rasa, wanda ake zarginsa da yin sama da fadi da su.

Sai dai duk kokarin Aminiya don jin ta bakin Kwamadan Na Dala ya ci tura, kasancewar bai amsa kiran wayar da aka yi masa ba haka kuma bai mayar da sakon kar-ta-kwanan da aka aike wayarsa ba.

Aminiya ta tuntubi Hedikwatar Hukumar Hisbah akan lamarin inda jami’in Hulda da Jama’a na hukumar Malam Lawan Fagge ya ce ba zai iya cewa komai ba kasancewar hukumar na gudanar da bincike akan lamarin yanzu haka.

Ya kara da cewa tuni Hukumar ta gayyaci kwamadan don amsa tambayoyi kuma yanzu haka suna ci gaba da gudanar da bincike.