✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An zargi jami’an Hukumar Shigi-da-Fici da yi wa makiyaya tara a Jigawa

Fulani makiyaya a Jihar Jigawa sun koka kan yadda jami’an Hukumar Shigi-da-Fici suke bin su da motoci zuwa rugagensu da cikin daji suna yi musu…

Fulani makiyaya a Jihar Jigawa sun koka kan yadda jami’an Hukumar Shigi-da-Fici suke bin su da motoci zuwa rugagensu da cikin daji suna yi musu tara.

 Shugaban Kungiyar Miyatti Allah Alhaji Sa’idu Gagarawa ya ce jami’an Hukumar Shigi-da-Ficin suna uzzura wa Fulani suna amsar abin da ya kai har Naira dubu bakwai a matsayin tara kuma idan babu kudi su kama dabobin makiyaya su saka a mota su tafi da su a madadin kudin.

Alhaji Sa’idu Gagarawa ya ce an yi wa Fulani fiye da 300 irin wannan tara ta kwace, lamari da ya jawo suka rika kaurace wa fita kiwo, amma sai jami’an suka koma bin su har rugagensu.

Shugaban Kungiyar Fulanin ya ce sun bincika a jikin takardun da ake bai wa Fulanin ba a rubuta kudin tarar da ake yi musu.

Shugaban Hukumar Shigi-da-Fici ta Jihar Alhaji Muhammed Kiyari ya ce ya samu labarin wadansu jami’ai masu kayan sarki suna yi wa Fulani tara, ya sa a yi bincike a kan lamarin kuma za su hukunta duk wanda aka samu da hannu a badakalar.

Shugaban ya ce yana da tabbacin cewar ba ma’aikatansa ba ne amma za su gudanar da tsattsauran bincike da zarar sun kammala za su kira taron manema labarai su fada wa duniya matsayinsu a kan wadanda suka samu da hannu a cikin lamarin.

Ya ce hukumar ba ta tura kowa ba, kuma ba ya da masaniya a kan yadda wadancan batagari suke amfani da kayan sarki suna bata wa hukumar suna. Ya ce duk wanda suka kama muddin jami’in hukumar ne za su ladabtar da shi.

Ya ce su aikinsu shi ne su duba wadanda suka shigo kasa babu izini su yi waje da su, amma babu inda doka ta ce a bi Fulani ’yan kasa har rugarsu a yi musu tara a ba su wani katin da ake bai wa bakin da ba ’yan kasa ba, “Duk wanda muka kama da irin wannan laifin zai dandana kudarsa,” inji shi.