Gwamnatin Ghana ta sanar da zaftare kashi 30 cikin 100 na albashin dukkanin masu da rike da mukaman siyasa a tarayyar kasar.
Wannan dai daya ne daga cikin matakan da gwamnatin ta bullo da su na rage matsin tattalin arziki da kasar ke fuskanta.
- Garba Shehu ya tura sakon daukar aikin da aka rufe tun 2021
- Shekara 30 Atiku na neman kujerar shugaban kasa
Fadar Gwamnatin Kasar ce ta sanar da hakan cikin wani sako da ta wallafa ranar Laraba a shafinta na Twitter, tana mai tabbatar da amincewar Shugaba Nana Akufo Addo a kan matakin.
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa, sauran matakan da gwamnatin ta Ghana ta dauka sun hada da bude duk iyakokin kan tudu na kasar cikin makonni biyu, wadanda suka kasance a rufe tun bayan bullar annobar Coronavirus karon farko a shekarar 2020.
Haka kuma, Babban Bankin Ghana ya rubanya darajar kudin ruwa da kashi 17 cikin 100, inda a yanzu farashin rancen kudi a banki zai karu.
Bugu da kari, gwamnatin za ta cusa karin dala biliyan biyu a cikin tattalin arzikin kasar domin farfado da takardar kudi na Cedi wanda a watannin baya bayan nan darajarsa ke faduwa a kasuwar canjin kudi.
A nan gaba kadan ake sa ran Ministan Kudi na Ghana, Ken Ofori-Atta zai yi jawabi dalla-dalla lan matakan da gwamnatin ta gindaya domin dakile kalubalen tattalin arziki da ake fuskanta a halin yanzu.
Majalisar Zartarwar Ghana ta kuma yanke shawarar rage alawus-alawus da ake biyan mambobinta duk wata da kashi 20 cikin 100 har zuwa karshen shekarar nan da muke ciki.