✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An zafafa kamen mabarata da karuwai a Abuja

Ana kuma kai samame a sansanonin mata masu zaman kansu dare da rana.

Ma’aikatar Kula da Babban Birnin Tarayya, Abuja, ta zafafa kamen da take yi wa masu zama ko yawon bara a kwarya da kuma kewayen birnin Abuja.

Aikin da Daraktan Kula da Walwalar Jama’a na Ma’aikatar Malam Sani Amar yake jagoranta, ya hada da kama masu zama a gidajen karuwai da kuma yara masu talla.

Aminiya ta gano cewa Daraktan tare da jami’an hukumar da suke samun rakiyar jami’an tsaro, suna yin dirar mikiya ne a wuraren da mabarata suke zama don yin bara inda a ke kama su.

Haka kuma jami’an suna kai samame a sansanonin mata masu zaman kansu dare da rana suna kama su.

Aminiya ta ga yadda aka kama wadansu masu bara a ranar Litinin da ta gabata, inda aka kai su Sakatariyar Hukumar.

Daga bisani Daraktan ya nemi jin ta bakin wadanda aka kama ciki har da wani matashi mai matsalar makanta wanda ya zubar da kwalla tare da neman a yi masa afuwa inda ya dauki alkawarin kiyaye ka’idar hukumar.

Sai dai Daraktan ya ce za a kai wadanda aka kama zuwa cibiyoyoyin ba da horon sana’a da nufin ba su horo, inda za a kula da abinci ko kuma a ba da belin su idan suka cika sharuddan da suka hada da alkawarin daina yin bara a birnin.

Da yake yi wa wakilinmu bayani kan wadansu da hukumar ta kama a bayabayan nan, Daraktan ya ce har da wata baiwar Allah da suka kama da ke yin bara a yankin Gwarimpa, Abuja da aka samu da kudi sama da Naira dubu 600 a jikinta, amma take zama cikin kunci maimakon ta yi sana’a ko kasuwanci da kudin.

Ya ce an yi amfani da kudin wajen kula da ita tare da biya mata kudin mota zuwa jiharta ta asali. Kuma ya ce sun kama wata budurwa da take sanya bandeji a kan mamanta da sunan cutar kansar mama tana yin bara.

“Mun kai ta Babban Asibitin Maitama, Abuja inda ta nuna tirjiya ga jami’an kiwon lafiya mata a loakcin da suka yi yunkurin yaye bandejin da ke kan maman, sai dai a karshe an gano cewa matsalar ta bogi ce, lafiyarta kalau babu wani ciwo a tare da ita,” inji Daraktan.

Babban jami’in ya yi bayani a kan yadda suka kama wadansu yara mata kanana da suke yawon tallan gyada, amma sai su yada zango a dakunan maza, kamar yadda ya ce sun kama wadansu daga cikinsu a cikin wannan yanayin.