A ranar Litinin da ta gabata ne Hukumar shirya kwallon kafa a Fotugal ta zabi kocin kulob din Chelsea da ke Ingila dan asalin Fotugal Jose Mourinho a matsayin Gwarzon Kocin karni na kasar a lokacin da hukumar ta yi bikin cika shekara 100 da kafuwa. Wannan karramawa ta sa kocin ya zama babu kamarsa a tsawon shekara 100 a tarihin kasar.
dan shekara 51, Jose Mourinno ya bayyana matukar farin cikinsa a kan zaben da aka yi masa kuma ya ce ko shakka babu nasarar da ya samu da kulob din FC Porto ce a shekarun baya sun taimaka matuka wajen wannan karramawar da aka yi masa.
“A gaskiya nasarar da na samu da kulob din FC Porto ce ta fi muhimmanci a rayuta ta, don nasara ce da na samu tare da fiye da rabin ’yan kwallon Fotugal a lokacin da nake horar da kulob din a wancan lokaci. Ba zan taba mantawa da yadda na lashe kofin zakarun kulob-kulob na Turai (UEFA Champions League) a karo na farko a kulob din ba, a lokacin da muka buga wasan karshe da ’yan wasa tara kacal bayan an ba biyu daga cikin ’yan kwallona katin kora. Sannan a shekarar ce na lashe kofin gasar rukuni-rukuni na Fotugal da kuma kofin kalubale (FA) kafin daga bisani na bar Fotugal zuwa kasashen Ingila da Italya da Sifen don cigaba da horarwa.” ya fadi haka a lokacin da yake hira da manema labarai.
Sannan a wajen bikin karramawar ce kuma aka zabi shahararren dan kwallon kulob din Real Madrid da ke Sifen Cristiano Ronaldo a matsyain Gwarzon dan kwallon karni na kasar. Ronaldo ya shigan gaban tsofaffin ’yan kwallon da suka fafata a gasar ce da Eusebio da Rui Costa da Coluna da kuma Luis Figo.
Idan ba a manta ba Ronaldo ne ya lashe Gwarzon dan kwallon Duniya a bana a makon jiya.
Hukumar kwallon kafa ta Fotugal ta ce ta zabi Ronaldo a wannan matsayi ne don ta yi amanna babu kamar dan kwallon a tsakanin shekaru 100 da kafuwar hukumar kawo yanzu.