✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An zabi Mfon Udoh a matsayin Gwarzon dan kwallon Najeriya

Mfon Udoh, dan kwallon kulob din Enyimba ne aka zaba a matsayin Gwarzon dan kwallon Gasar Rukunin Firimiya ta Najeriya a ranar Litinn da ta…

Mfon Udoh, dan kwallon kulob din Enyimba ne aka zaba a matsayin Gwarzon dan kwallon Gasar Rukunin Firimiya ta Najeriya a ranar Litinn da ta wuce. 

Ya samu wannan nasara ce a wani zaben da aka yi a Legas a ranar 15 ga watan nan da muke ciki bayan ya doke abokin takararsa da shi ma yake buga kwallo a kulob din Enyimba watau Bobby Sokari. Mfon Udoh ne ya zama dan kwallon da ya fi zura kwallo a raga a gasar rukunin firimiya ta Najeriya a bana bayan ya zura kwallaye 23.
Mfon Udoh, ya bayyana farin cikinsa a kan wannan zabe da aka yi masa kuma ya sha alwashin cigaba da nuna kwazo a kakar wasa mai zuwa.
Udoh, mai kimanin shekara 22, yana da burin ya tsallake zuwa kasashen ketare musamman Nahiyar Turai don ganin ya samu kulob din da zai cigaba da yin wasa.
“Duk wanda ya yi na daya a yawan zura kwallaye a gasar rukunin Najeriya yakan tsallake zuka kasar waje idan ya samu kulob don haka ni ma ina da burin yin haka”, inji shi a lokacin da ake hira da shi.
Duk da yake dan kwallon ne ya fi yawan zura kwallaye a raga a gasar, amma ba kulob dinsa na Enyimba na ya lashe kofin ba. Kano Pillars ce ta lashe kofin a karo na uku a jere, yayin da na Enyimba ya kasance na biyu.