Cibiyar Aikin Jarida Na Binciken kwa-kwaf ta Wole Soyinka, ta karrama Shugaban kamfanin Media Trust Limited, Malam Kabiru Yusuf, inda ta ba shi kambin girmamawa, a matsayinsa na mai gudaar da aikin jarida cikin inganci da nagarta.
Shugabar cibiyar, Motunrayo Alaka ce ta sanar da kyautar a ranar Talatar da ta gabata kuma za a gudanar da bikin mika kambin ne a ranar Jumu’a ta makon gobe, a yayin bikin ranar bayar da kyautar ’yan jarida masu binciken kwa-kwaf karo na 11, wanda zai gudana a Legas.
An zabi Malam Kabiru Yusuf ne saboda yadda ya dage wajen tabbatar da ganin cewa an yi aiki mai kyau a fannin aikin jarida kamar yadda za a iya gani a jaridun kamfanin Media Trust.
Kamfanin Media Trust Limited ne ke buga jaridun Aminiya da na Daily Trust da kuma sabuwar mujallar Kilimanjaro.
Haka nan kuma za a bayar da kyautar yaki da cin hanci da rashawa na cibiyar PPDC.
PPDC wata kungiya ce ta kare hakkin dan Adam, wadda aka kirkiro domin kara bayar da dama ga mutane, domin su shiga cikin harkar gwamnati domin tabbatar da gaskiya da rikon amana a bangaren gwamnati da jama’a masu zaman kansu.
Haka nan kuma za a bayar da kambin dan jarida mai binciken kwa-kwaf na wannan shekarar a wajen bikin bayar da kyaututtukan.
Labaran da aka zaba domin wannan kyauta, an zakulo su ne daga jerin labarai 125 da aka turo kuma alkalai wadanda suke da tarihi mai kyau a bangarorin aikin jarida daban-daban suka tantance.
Wadanda suke lashe gasar, za su karbi kyautar kudade da kuma kambi na musamman wanda ke dauke da suna da dalilin bayar da ita, kuma za su samu damar yin tafiya zuwa wasu kasashen duniya domin karo ilimi a shekara mai zuwa. Sannan kuma duk wanda ya samu shiga cikin wadanda za a zaba na karshe, zai samu takardar shaida ta aiki mai kyau.
An kirkiro kyaututtukan ne domin karkafa aikin jarida bangaren binciken kwa-kwaf tare da bayar da gudunmuwa ga yaki da cin hanci da rashawa.
An zabi Malam Kabiru Yusuf a matsayin gwarzon dan jarida mai nagarta
Cibiyar Aikin Jarida Na Binciken kwa-kwaf ta Wole Soyinka, ta karrama Shugaban kamfanin Media Trust Limited, Malam Kabiru Yusuf, inda ta ba shi kambin girmamawa,…