Majalisar Dokokin Jihar Oyo ta amince da sunan Kwamishinan Shari’a na jihar, Bayo Lawal, a matsayin sabon Mataimakin Gwamnan jihar.
’Yan majalisar sun amince da sunan nasa ne ranar Litinin, bayan Gwamnan Jihar, Seyi Makinde ya aike da shi domin neman amincewarsu.
- An fara zafin da ba a taba yin irinsa ba a tarihin Landan
- An haramta amfani da Adaidaita Sahu daga karfe 10 na dare a Kano
Aminiya ta rawaito cewa da sanyin safiyar Litinin din ce Majalisar ta tsige Mataimakin Gwamnan Jihar na da, Injiniya Rauf Olaniyan.
An tsige shi ne bayan mambobin kwamitin mutum bakwai da aka kafa domin binciken shi karkashin Babban Jojin jihar, Munta Abimbola, ya gabatar da rahotonsa.
Rahoton dai ya tabbatar da zarge-zargen da ake yi wa Rauf kan aikata ba daidai ba.
Rahoton, wanda aka gabatar a zauren majalisar ranar Litinin ya ce an sami tsohon Mataimakin Gwamnan da aikata dukkan laifukan da ake tuhumarsa da aikatawa.
Dukkan ’yan majalisar mambobin jam’iyyar su 23 sun amince da rahoton kwamitin.
Bayanai na nuni da cewa majalisar ta fara yunkurin tsige shin ne tun lokacin da ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP mai mulkin jihar zuwa ta APC.