✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An zabi Andre Iniesta a matsayin Kyaftin din FC Barcelona

A ranar Litinin da ta gabata ne ’yan kwallon kulob din FC Barcelona da ke Sifen suka gudanar da zabe a asirce na wanda zai…

A ranar Litinin da ta gabata ne ’yan kwallon kulob din FC Barcelona da ke Sifen suka gudanar da zabe a asirce na wanda zai gaji tsohon dan kwallonsu dabi a matsayin kyaftin. Idan za a tuna dabi dai ya bar kulob din ne a karshen kakar wasa ta bana, inda ya koma katar don cigaba da kwallo.  ’Yan kwallo biyu ne suka fafata don neman wannan matsayi, watau Andre Iniesta da kuma Lionel Messi.
Jim kadan da gudanar da zaben ne sai mahukunta kulob din Barcelona suka bayar da sanarwar Andre Iniesta a matsayin wanda ya lashe zaben, don haka shi ne sabon kyaftin.  
Lionel Messi ne ya kasance a matsayin mataimakin kyaftin, watau a duk lokacin da ba Inietsa a cikin fili, to shi zai maye gurbinsa.  Sai kuma aka zabi Sergio Buskuets a matsayin na uku sannan Jabier Macherano kuma a matsayi na hudu.
Sai dai mahukunta kulob din sun ce kafin a tabbatar wa Ineista da sauran wadanda aka zaba a sabon mukaman sai an nemi amincewar kocin kulob din Luis Enrikue tare da masu taimaka masa.
A kakar wasa ta bara, Gerard Pikue ne ya kasance a matsayin na hudu amma a wannan karo sai Jabier Mascherano ya mare gurbinsa.
Ineista ne ya fi kowane dan kwallo tsufa a kulob din FC Barcelona don tun cikin watan Oktoban 2002 ne ya koma kulob din.