✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi zanga-zangar cika shekara 3 da hambarar da gwamnatin Al-Bashir a Sudan

Sai dai masu zanga-zangar sun ce babu bambanci tsakanin gwamnati mai ci da ta Al-Bashir

Daruruwan masu zanga-zanga sun fantsama titunan Khartoum, babban birnin Sudan don murnar cika shekara uku da hambarar da gwamnatin Shugaba Omar Al-Bashir da kuma nuna adawa da mulkin soja a kasar.

Wasu sojoji ne dai suka hambarar da gwamnatin tasa bayan shafe shekara 30 a kan mulkin kasar a 2019.

Sojojin dai sun shafe tsawon wata 19 suna mulki tare da wasu fararen hula.

Sai dai yarjejeniyoyar ta zo karshe a watan Oktoban 2021, lokacin da wasu sojojin daga cikin gwamnatin kasar, karkashin Janar Abdul Fattah Al-Burhan suka sake yin juyin mulki.

Hakan dai ya yi sanadiyyar jefa kasar cikin rikicin siyasa da na tattalin arziki.

“Hambarar da gwamnatin Al-Bashir ba yana nufin an gama cin nasara ba ne, saboda gwamnatin Janar Al-Burhan da ta Al-Bashir kamar Danjuma ne da Danjummai. Za mu kawar da ita ma sannu a hankali mu dawo da Dimokuradiyya,” inji Ahmed Ibrahim, wani matashi daga cikin masu zanga-zangar, kamar yadda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters a Khartoum.

Masu zanga-zangar dai sun toshe manyan hanyoyin birnin, sannan suka rika kona tayoyi suna buga ganguna tare da rera wakokin nuna adawa da gwamnati.

Ana dai gudanar da zanga-zangar ce duk da rubdugun da jami’an tsaro suka yi a kan mutane, wanda ya yi sanadin kashe mutum 94.

Sai dai jami’an tsaro sun musanta kashe fararen hula.

Masu zanga-zangar dai sun yi buda-bakinsu a kan titunan birnin bayan kammala azumi, kamar yadda suka yi a makon da ya gabata.