Wasu matasa sun gudanar da zanga-zanga a kan titin Hadeja Road kusa da Kwanar Dakata don nuna tirjiya ga dokar hana baburan Adaidaita Sahu bin wasu titunan Jihar.
Matasan da suka hada da matuka baburan da kuma mazauna yankin da suka hada da daliban makaranta da ’yan kasuwa da sauran jama’ar yankin inda suka rufe kan titin suka hana sauran ababen hawa bi.
Baya ga haka kuma matasan sun yi ta ihu tare da furta kalaman Allah-wadai da matakin na Gwamnatin Jihar ta Kano.
Wasu daga cikin masu zanga-zangar sun yi amfani da wannan dama wajen jifan jami’an tsaro tare da ababen hawansu da duwatsu.
Haka kuma, ana cikin zanga-zangar sai ga wasu daga cikin motocin da Gwamnatin ta samar da suka maye gurbin baburan da ake yi wa lakabi da Kanawa Bus Service sun iso daidai wurin da ake zanga-zangar, nan da nan kuwa matasan suka fara jifan motocin da duwatsu inda suka farfasa gilasan motocin tare da yi wa fasinjojin da ke ciki rotse.
Sai dai kasancewar akwai isassun jami’an tsaro akan titin wanda aka ajiye su don ko-ta-kwana sun yi kokarin kwantar da tarzomar inda suka kama wasu daga cikin matasan wadanda suke zargin su ne da alhakin assasa zanga-zanga tare da tunzura matasan.
Wasu daga cikin daliban makarantua da ke yankin sun shaida wa Aminiya cewa sun shiga wannan zanga-zangar ce saboda rasa abin hawan da zai mayar da su gidajensu.
Wani dalibai mai suna Ahmad Ali ya ce, “Kasancewar jarrabawa muke yi ana tashinmu da karfe 11:00 na safe, to amma saboda rashin baburan Adaidaita Sahu gashi har yanzu karfe 12:30 muna kan titin, babu motocin da aka ce su za su dauke mu.
“A gaskiya Gwamnati ba ta kyauta mana ba. Kamata ya yi gwamnati ta yi abin a hankali ba wai kawai cikin kankanen lokaci ace za a kawo doka ta fara aiki ba.”
Shi ma wani matashi da ke cikin masu zanga-zangar wanda ya ki bayyana sunansa, ya shaida wa Aminiya cewa sun yi zanga-zangar ne don sun rasa abin hawan da zai biya musu bukatunsu na sufuri.
“Kin San nan akwai Kasuwar Yankaba to muna yin amfani da baburanAdaidaita Sahu wajen daukar mana kayan gwari da muka saya zuwa wuraren kasuwancinmu, amma kin ga yau saboda wannan doka mun rasa abin da zai daukar mana kayan. Ga shi har rana ta yi,” inji shi.
Aminiya ta tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, wanda ya ce ba shi da masaniya a kan abin da ke faruwa.
Sai dai ya ce da zarar ya bincika zai tuntunbe mu. Amma har zuwa lokacin hada wannan rahoton ba mu sami kira daga wajenshi ba.