Dubban matasa ne suka fito kan tituna a Jihar Jigawa don nuna rashin amincewarsu da abin da suka bayyana a matsayin rashin adalci a tsarin daukar malamai aiki.
Masu zanga-zangar sun yi zargin cewa jarabawar daukar aiki da hukumar ilimin bai-daya ta jihar ke yi na hana su samun mukamai.
- Budurwa ta mutu tana tsaka da saduwa da ‘Dan Yahoo’
- Kano: Lauyoyin Arewa 200 sun lashi takobin taimakon Abba a Kotun Koli
Hakan na zuwa ne bayan gwamnan jihar, Umar Namadi ya amince da daukar malamai 3,000 domin cike gibin da aka samu a fadin jihar.
Matasan sun taru ne a cibiyoyin jarabawar da Hukumar Kula da Ilimin Bai-daya ta Kasa (SUBEB) ta ware, inda suka bayyana takaicinsu a yayin zanga-zangar.
A cewarsu, sun kasance suna aiki a karkashin shirin J-Teach a matsayin malamai na wucin gadi kuma sun yi zargin shirin gwamnati na daukar malaman dindindin yana cike da kurakurai.
Yayin da wasu daga cikin malaman da suka gudanar da zanga-zangar suka yi ta nuna rashin amincewarsu da jarabawar , wasu kuma sun yi ikirarin cin jarabawar.
Sai dai gwamnatin jihar ta ce tana yin gwajin ne domin tabbatar da cancantar malaman da kuma inganta bangaren ilimi a jihar.