Daruruwan mutane ne suka yi zanga-zangar adawa da komawar tsohon Sarkin Spain Juan Carlos gida, wanda ya koma kasar daga Hadaddiyar Daular Larabawa, bayan shafe shekara biyu da gudun hijira.
Kakakin gwamnatin Spain, ya ce akalla mutane 300 suka gudanar da zanga-zangar kusa da fadar sarkin da ke birnin Madrid.
- Mamakon ruwan sama ya hana kammala bikin gasar ninkaya a Legas
- ‘Za a sami ambaliyar ruwa a Kananan Hukumomi 233 na Najeriya’
Sun gudanar da zanga-zangar ne domin nuna bacin ransu saboda zargin cin hanci da kuma halarta kudaden haramun da ake masa.
A ranar Litinin ake saran tsohon sarkin zai ziyarci dansa, Sarki Felipe na 6 kafin komawa Daular Larabawa, inda ya ke ci gaba da zama.
Gwamnatin Firaminista Pedro Sanchez na ci gaba da dakon bayanai kan dalilin da ya sa Juan Carlos, ya sauka daga karaga a 2014 domin nada dansa.