Kwamitin yaki da cin zarafin mata a Jihar Bauchi tare da hadin gwiwar ma’aikatar harkokin mata da ci gaban kananan yara, sun ce akalla mata 226 ne aka yi wa fyade cikin shekara uku a jihar.
Shugabar kwamitin kuma uwargidan gwamnan jihar, Hajiya Aisha Bala Mohammed, ce ta bayyana hakan.
- Buhari ya bar bashin tiriliyan 1.5 a ma’aikatar ayyuka —Umahi
- Kamfani zai samar da lantarki daga hasken rana ga rukunin gidaje a Kano
A’isha ta shaida wa gwamnan jihar, kwamitin ya yi nasarar kafa cibiyar tuntuba kan cin zarafin mata, kuma cibiyar ta duba lafiya kyauta ga wadanda suka kubuta daga cin zarafi.
Ta shaida wa gwamnan cewa, “An kammala cibiyar tare da samar da kayan aiki. Kwamitinmu kuma yana aiki da kuma tallafa wa wadanda aka cutar.
“Kwamitin tare da hadin gwiwar ma’aikatar harkokin mata da ci gaban kananan yara, sun shiga tsakani a batutuwa 226 da suka shafi fyade, wadanda galibi suka shafi kananan yara; laifuka 68 na tashin hankali, 47 na cin zarafin yara, sai 53 da suka shafi iyali, karfafa zamantakewa da tattalin arziki.”
Gwamna Bala Mohammed ya gode wa uwargidansa da kwamitin bisa kokarinsu wajen magance matsalar cin zarafin mata a jihar.
Gwamnan ya ce, “A Bauchi, abin takaici, wasu masu tsafi… sun sanya wannan mummunar dabi’a ta zama ruwan dare a cikinmu.
“A matsayinmu na al’umma, wannan ya saba wa dabi’unmu, al’adunmu, har ma da addininmu a matsayinmu na Musulmi da Kirista.”