Rundunar ’yan sanda ta bayyana cewa an yi wa wata yarinya ’yar shekara biyu fyade har lahira a Ƙaramar Hukumar Ningi ta Jihar Bauchi.
Kakakin ’yan sanda a jihar Bauchi, Ahmed Mohammed Wakil, a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Talata, 5 ga Nuwamba, 2024.
Ya ce an kai rahoton aikata laifin ne a hedikwatar ’yan sanda da ke Ningi bayan “an gano gawar wata ’yar shekara biyu a gefen wani masallaci da ke kan titin Deneva, a Ƙaramar Hukumar Ningi, da alamun fyaɗe.
“Bayan samun rahoton an tura jami’an tsaro zuwa wurin suka ɗauke gawar zuwa Babban Asibitin Ningi, inda rahoton likita ya tabbatar da cewa ta samu munanan raunuka a sakamakon fyaɗen, wanda ya yi sanadin mutuwarta.”
- DAGA LARABA: Tarihin Almajirci a kasar Hausa da yadda yake a da
- Babban layin lantarkin Nijeriya ya sake daukewa
Wakil ya ce, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Bauchi, Auwal Musa Mohammed, ya yi tir da lamarin, inda ya bayyana shi a matsayin babban laifi, ya kuma umarci babban ofishin ’yan sanda na shiyyar Ningi da ya kamo waɗanda suka aikata laifin tare da gurfanar da su a gaban kuliya.
“Ya kuma yi kira ga iyaye da masu kula da yara da su tabbatar da tsaron ’ya’yansu, kar su bari su riƙa yawo a kan tituna.
“Rundunar tana neman taimakon jama’a da duk wani bayani mai amfani da zai taimaka wajen kamawa da hukunta waɗanda suka aikata laifin.”