Sakataren Gwamnatin Tarayya kuma shugaban Kwamitin Kar-ta-kwana da Shugaban Kasa ya kafa kan yaki da COVID-19, Boss Mustapha ya ce sama da ’yan Najeriya miliyan daya ne aka yi wa allurar rigakafin cutar.
Ya bayyana hakan ne yayin wani taron tattaunawa a kan rigakafin cutar na yankin Arewa ta Tsakiya da kwamitin ya shirya a Lafiya babban birnin jihar Nasarawa ranar Laraba.
- Majalisar Dattawa ta amincewa gwamnati ciyo bashin $1.5bn da €995
- Ba mu tattauna batun Pantami a taron Majalisar Zartarwa ba – Lai Mohammed
Ya ce taron na daya daga cikin irin shirye-shiryen da ake yi n a wayar da kan jama’a a kan ci gaban da ake samu kan rigakafin da aka fara a farkon watan Maris.
Boss Mustapha ya ce burin kwamitin nasa shine ya yi wa kaso 70 cikin 100 na ’yan Najeriya rigakafin nan da shekaru biyu masu zuwa.
Shi kuwa Ministan Lafiya Osagie Ehnire cewa ya yi ma’aikatarsa na aiki kafada da kafada da dukkan masu ruwa da tsaki wajen ganin Najeriya ta amfana da alluran cutar wadanda Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta amince da su.
Shugaban Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Kasa (NPHCDA), Faisal Shuaib da Gwamnan jihar Nasarawa sun ce an shirya taron ne da nufin tabbatarwa da shugabannin addinai da masu rike da sarautun gargajiya cewa allurar ba ta da wata illa ga ’yan Najeriya.
Taron dai shine irinsa na farko da ake sa ran gudanarwa a dukkan shiyyoyin siyasa shida na kasar nan.