✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘An yi wa ’yan bindiga tayin kudi don kar su saki Daliban Jangebe’

Gwamnan Zamfara ya ce daliban su 279 ne kuma wasu sun yi wa masu garkuwa da su tayin kudi don kar su sake su.

Gwamnan Jihar Zamfara, Muhalli Bello Matawalle ya yi zargin wasu miyagun mutane sun yi wa ’yan bindiga romon baka cewa za su ba su kudi don kar su saki dalibai mata da suka yi garkuwa da su daga Makarantar GGSS Jangebe.

Da yake bayyana cewa dalibai 279 ne aka yi garkuwa da su aka kuma ceto daga ’yan bindiga, Matawalle ya ce a yayin da Gwamnati ke tattaunawa da ’yan bindigar don su sako su, wasu sun zaga ta bayan fage suna zuga ’yan bindigar cewa su za su ba su kudi kar su saki daliban.

Gwamnan, a bayaninsa ga daliban su 279 bayan isar su Gidan Gwamnatin Jihar, ya ce tuni jami’an tsaron DSS da Sojoji da ’yan sanda sun fara aikin bankado wadannan masu hana ruwa gudun.

Ya kuma yi kashedi ga masu zuga ’yan bindiga a jihar da su shi taitayinsu ko kuma su yaba wa aya zaki.

“Kwanana hudu ban rintsa ba, muna ta fadi-tashin ganin an sako daliban ga iyalansu.

“Mun yi amfani da dabarun soji da na farar huka, kuma su suka fi mana amfani, ba don haka ba da ba a sako daliban ba,” inji shi.

Matawalle ya roki iyaye cewa kar su sake harin ya sanyaya musu gwiwar barin ’yan’yan su halarci makarantu don samun ilimi.

Ya ce gwamnatin jihar na yin iya kokarinta don kawo karshen ayyukan ’yan bindiga da suka addabi Jihar da ke yankin Arewa maso Yamma a Najeriya.

Da sanyin asubahin ranar Talata ne daliban sanye da shuddan hijabai suka isa Gidan Gwamnatin Jihar da ke Gusau a cikin motocin safa bayan masu garkuwar sun sako su.

A daren Juma’a ne ’yan bindiga suka kai wa makarantar mata zalla wato GGSS Jangebe hari suka yi awon gaba da daliban daga dakunan kwanansu.

Harin makarantar Jangebe shi ne irinsa ba biyu a wata guda —Fabrairun 2021 a Najeriya.

Kafin shi mahara sun yi dirar mikiya a makarantar samari zalla ta GSC da ke garin Kagara a Jihar Neja inda suka yi awon gaba da dalibai da ma’aikata da iyalansu a cikin duhun dare.