✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi wa soja 123 karin girma

Rundunar Sojan Najeriya ta amince da yi wa soja 123 da suke da mukamin manjo karin girma zuwa mukamin laftanar kanar da kuma masu mukamin…

Rundunar Sojan Najeriya ta amince da yi wa soja 123 da suke da mukamin manjo karin girma zuwa mukamin laftanar kanar da kuma masu mukamin laftanar kanar zuwa kanar.
Mai Magana da Yawun Rundunar, Birgediya Janar, Sani Usman ya bayyana cewa soja 66 masu mukamin laftar kanar an yi musu karin girma zuwa mukamin kanar, sai kuma soja 57 masu mukamin manjo an yi musu karin garima zuwa laftar kanar.
Ya ce karin girma ya auku ne sakamakon amincewar hukumar karin girma ta soja ta 3 da ta 4 kuma karin girma ya shafi dukkannin jami’an da suka cancanta.