Wasu matasa sun yi wa Minista a ma’aikatar Babban Birnin Tarayya Abuja, Hajiya Ramatu Tijjani Aliyu ihun ‘ba ma so’ a Abuja.
Rahotanni sun ce matasan, wadanda galibinsu ’yan siyasa ne sun yi mata ihun ne lokacin da ake tsaka da bikin raba takardun shaidar lashe zabe ga wadanda suka yi nasara a zaben Kananan Hukumomin Abuja, wanda Kwamishinan Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta a yankin, Alhaji Yahaya Bello, ya jagoranta.
- An sace tsohuwa mai shekara 70 da wasu mutum 10 a Taraba
- Sabon Kwamishinan ’Yan Sanda ya lashi takobin ganin bayan ’yan bindiga a Katsina
An dai tsara Ministar za ta yi jawabi ne a wajen, amma mutanen suka fusata, lokacin da ta ba INEC shawarar ta samo wata hanyar da mutane za su rika jefa kuri’a ta hanyar amfani da wani kundi.
Sai dai a nan take mutane suka fara yi mata ihu suna cewa ‘karya ne, ba ma so’.
Amma ko da Ministar ta yi kokarin yi musu jawabi kan abin da take nufi, sai suka ci gaba da ihun, lamarin da ya sa hatta Sanata mai wakiltar Abuja a Majalisar Dattawa wanda shi ma yake wajen ya kama hanya ya tafi.
Aminiya ta lura cewa hatta jami’an tsaron da ke wajen sai da lamarin ya fi karfinsu, inda suka kasa han fusatattun mutanen yin ihun.
Hakan ya sa ala tilas Ministar ta ajiye abin maganarta, sannan ta koma cikin rumfar manyan baki ta gaisa da su, kafin daga bisani ita ma ta bar wajen.
Kwamishinan hukumar ta INEC, Alhaji Yahaya Bello daga bisani ya ba da takardun shaidar lashe zaben ga Shugabannin Kananan Hukumomin Abuja da Kewaye da Kwali da Gwagwalada da Bwari da kuma Kuje.
Kwamishinan ya taya zababbun Shugabannin murnar lashe zaben tare da kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su hada gwiwa da INEC wajen ganin an yi zabukan 2023 cikin lumana.