✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka yi wa mijin tsohuwar Minitsa kisan gilla

Bidiyon kisan gillar ta nuna su suna birgima a kasa bayan an harbe su.

’Yan bindiga sun harbe mijin tsohuwar Ministar Sadarwa da Yada Labarai, Farfesa Dora Akunyili, Dokta Chike Akunyili

Wani bidiyon kisan gillan da aka yada a kafafen sada zumunta ya nuna mamacin tare da wani a kwance cikin jini a bainar jama’a suna birgima bayan an yi musu luguden wuta.

An ji wani wanda ya shaida aukuwar lamarin yana cewa, “Allah Ya karya wannan shaidanin da rundunarsa.”

Maharan sun kashe Dokta Chike Akunyili tare da wasu mutum bakwai ne ne a yankin Umuoji da ke Karamar Hukumar Idemili ta Arewa a Jihar Anambra.

An hallaka Dokta Akunyili ne sa’o’i kadan bayan ya halarci taron karrama matarsa, Farfesa Dora Akunyili, wadda kungiyar tsoffin daliban Jami’ar Najeriya da ke Nsukka ta gudanar a harabar jami’ar.

Marigayiya Farfesa Dora Akunyili ita ce tsohuwa Shugaban Hukumar Kula da Ingacin Abinci da Magunguna ta Najeriya (NAFDAC).