✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An yi wa matashiya fyade sannan aka kashe ta a Edo

An jefar da gawarta a gefen titi bayan an kashe ta.

An yi wa wata matashiya mai shekara 20 fyade sannan aka kashe ta a gidanta a Jihar Edo.

An rawaito cewa lamarin ya faru a ranar 17 ga watan Yuli a Karamar Hukumar Etsako ta Gabas a jihar.

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin ’yan sandan jihar, SP Chidi Nwabuzor, ya ce, “’Yan sanda sun ziyarci wajen da aka jefar da gawarta, kuma an fahimci alamar fada da kuma raunin wuka a wurare daban-daban a jikinta.”

Ya ce bayan an caccaka wa matashiyar wuka a jikinta sai aka bar ta har rai ya yi halinsa, bayan da wasu da ba a san ko wane ba suka yi mata fyade.

Aminiya ta gano an cafke wani mai suna da ake zargi yana da hannu a kisan matashiyar.

An tsinci gawar matashiyar a yashe ne a kan titin Pandoponti a yankin Agenebode, bayan an kashe ta.

Kakakin ’yan sandan jihar, SP Chidi Nwabuzor, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce jami’ansu sun cafke wani da ake zargi na da hannu a kisan matashiyar, kuma yana taimakon ’yan da bayanan da suke nema.

Ya ce wani mai suna Paul, ya shigar da kara cewa an tsinci gawar ’yar uwarsa mai suna Precious Aigbokhode mai shekara 20, a kan titin Pandoponti.