✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi wa marasa lafiya da likitoci fashi a asibiti

’Yan fashin sun yashe likitoci da marasa lafiya da ke asibitin.

Wasu ’yan bindiga sun kutsa kai cikin wani asibiti da sanyin safiya, suka yi wa likitoci da marasa lafiya fashin kudade.

Lamarin ya faru ne a safiyar Talata, bayan ’yan fashin sun haura katangar asibitin mai suna Diete Koki a Jihar Bayelsa.

Daya daga cikin likitocin da ke aiki a lokacin da lamarin ya faru, Dokta Okeleghrl Awudumapu, ya shaida wa manema labarai cewar ’yan fashin sun tisa keyarsa ne bayan ya fito daga duba marasa lafiya.

Dokta Awudumapu, ya shaida wa manema labarai cewa maharan sun kwashe masa duk abin da yake da shi da na marasa lafiya da masu jinyarsu.

Da ya ke tabbatar da faruwar lamarin, daraktan asibitin, Dokta Emmanuel Fetepigi, ya bayyana damuwarsa da abin da ya faru, wanda ya bayyana a matsayin tsantsar rashin imani.

A cewarsa, hukumar gudanarwar asibitin za ta yi hadin gwiwa da Hukumar Lafiya ta Jihar Bayelsa don kauce wa sake faruwar hakan a gaba.

Mai gadin asibitin, James Benini, ya ce karo na biyu ke nan da barayi suke shigowa asibitin, inda ya ce a baya an taba shiga aka sace batirin injin janareton asibitin.

Kakakin ’yan sandan jihar Bayelsa, SP Asinim Butswat ya ce su dai ba su samu rahoton fashi a asibitin ba.