Hukumar Jin dadin Alhazan Jihar Kano ta gudanar da bitar Aikin Hajji aikace ga maniyyatan jihar domin su kara samun ilimi game da yadda ake gudanar da ibadar Hajji daki-daki.
Da ya ke bayani game da bitar a ranar Juma’a, Babban Sakataren hukumar Muhammad Abba Danbatta, ya bayyana cewa an tsara wannan bita ce don kara sanar da maniyyatan game da yadda matakan aikin Hajji suke.
- Rikici ya barke a hedikwatar Jam’iyyar APC
- Batanci ga Annabi: Shugabannin Musulman Indiya sun bukaci dakatar da zanga-zanga
“Bayan malaman bita sun gama koyar da maniyyatan akwai bukatar a koyar da maniyyatan Jihar a aikace domin ya bayyana cewa duk da cewa a tsawon shekaru biyu da suka gabata ba a gudanar da aikin Hajji ba, amma gwamnatin ba ta daina taimaka wa hukumar da kayan aiki ba.
Da ya ke nasa jawabin, Shugaban Kwamitin gudanar da bitar, Kwamandan Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Dokta Haruna Ibn Sina, ya bayyana cewa kimanin malamai 317 suka gudanar da bitar inda suka shafe tsawon watanni biyar suna koyar da maniyyatan game da rukunan ayyukan Hajji.
A nasa jawabin mai martabar Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, wanda ya samu wakilcin Wazirin Kano, Alhaji Sa’adu Gidado, ya yi kira ga maniyyatan da su dage sosai wajen yi wa kasa addu’a don samun bunkasar tattalin arziki da kuma zaman lafiya a fadin kasar gaba daya.
A jawabinsa, gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya kuma tunatar da maniyyatan cewa kotun Hukunta Alhazai ta Jihar Kano tana nan daram don hukunta Alhazan da suka nuna rashin da’a a kasa mai tsarki.
“Duk Alhajin da ya je kasa mai tsarki ya aikata abin da ba daidai ba, to idan ya dawo gida zai fuskanci hukunci daidai da laifin da ya aikata domin ba za mu yarda wasu tsirari su bata mana sunan jiha ba.”
Maniyyata da dama sun nuna jin dadinsu da gamsuwarsu game da wannan horarwa a aikace da aka yi musu.
Malam Suyudi Abdullahi Bichi, ya bayyana cewa a matsayinsa na sabon Alhaji ya samu karin ilimi akan abin da aka koya musu a wajen bita.
“Lokacin bita a karance aka koyar da mu, amma a yanzu da aka yi mana wannan gwajin mun fa’idantu sosai.”
Shi ma Shehu Sagiru Kurna daga Karamar Hukumar Fagge, ya bayyana cewa “A yanzu ji nake kamar na yi aikin Hajji na gama saboda abin da aka koyar da mu a yau.”
Malama Rukayya Saidu, daya ce daga cikin maniyyatan da suka fito daga Karamar Hukumar Kumbotso, ta shaida wa Aminiya cewa ta fa’idantu da wannan bita inda ta ce “Alhamdulillah da wannan bita ta gwaji da aka yi mana a yau. Ni ada ban fahimci wasu abubuwan ba sai da aka yi su a aikace a yau. Wallahi na ji dadi sosai.”
Malaman bitar Alhazai ne karkashin jagorancin Kwamandan Hukumar Hisbah ta Jihar Kano Dokta Harun Ibn Sina suka jagoranci yin bibitar a aikace, inda suka gudanar da manyan rukunan aikin Hajji a aikace da suka hada da Dawafi da Sa’ay da sauransu.