Rahotanni daga Jihar Kano da ke Arewacin Najeriya sun tabbatar da cewa, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da wasu manyan jami’an gwamnati sun karbi zagaye na biyu na rigakafin cutar Coronavirus.
A ranar Alhamis ce Gwamnan da kusoshin gwamnatin suka karbi rigakafin ta Astrazeneca COVID-19 vaccine kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Kasar NAN ya ruwaito.
- Biden ya yaba da yarjejeniyar tsagaita wuta a yakin Isra’ila da Falasdinawa
- EFCC ta kwato N1bn a hannun jami’in gwamnati
Da yake jawabi bayan karbar rigakafin, Ganduje ya yaba wa Ma’aikatan Lafiya na Jihar da kuma Shugabannin Addinai da Sarakunan Gargajiya dangane da gudunmuwar da suka bayar wajen ganin an cimma nasara a shirin bayar da rigakafin cutar Coronavirus a fadin Jihar.
Ya bayar da tabbacin cewa Gwamnatinsa za ta kawo karshen yaduwar cutar Coronavirus a fadin Jihar.
“Yanzu na karbi rigakafin Coronavirus zagaye na biyu, sannan kuma ina kira ga sauran al’ummar Jihar da su gabatar da kansu domin a yi musu rigakafin.
“Duk wanda ba a yi wa zagayen farko na rigakafin ba, ba ya cikin rukunin wadanda za su iya karbar zagaye na biyu na rigakafin.
“Ina mai tabbatar muku da cewa wannan shi ne mafarar karshen cutar Coronavirus a Jihar Kano,” a cewarsa.
Ganduje ya kuma nemi al’ummar jihar da su ci gaba da kiyaye matakan kariya na dakile yaduwar cutar kamar yadda mahukuntan lafiya suka shar’anta.
A nasa jawaban, Kwamishinan Lafiyar Jihar, Dokta Ibrahim Tsanyawa, ya ce mutum 3,968 cutar Coronavirus ta harba a Jihar Kano, kuma daga ciki 3,896 sun warke yayin da aka samu mutum 110 da suka riga mu gidan gaskiya.