✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An yi wa Buhari zanga-zanga a Landan

Wasu ’yan Najeriya mazauna kasar Birtaniya, sun yi wa Shugaba Muhammadu Buhari zanga-zanga a ranar Laraba inda suka nemi ya koma kasarsa. A safiyar Talatar…

Wasu ’yan Najeriya mazauna kasar Birtaniya, sun yi wa Shugaba Muhammadu Buhari zanga-zanga a ranar Laraba inda suka nemi ya koma kasarsa.

A safiyar Talatar da ta gabata ce Buhari ya tafi birnin Landan ganin Likitocinsa domin a duba lafiyarsa kamar yadda ya saba.

Rahoton da manema labarai na BBC suka ruwaito ya nuna cewa, wasu ’yan Najeriya a Birtaniya sun taru a kofar gidan Gwamnati Najeriya da ke birnin Landan kuma suka tare hanyar shiga.

Wasunsu sun dauki kwalaye masu dauke da sakon kiran Shugaban da ya koma gida Najeriya yayin da suka yi cincirindo a bakin Asibitin Wellington da ke birnin Landan.

Da dama daga cikin al’ummar Najeriya sun bayyana bacin ransu kan tafiiyar Buhari kasar Birtaniya domin a duba lafiyarsa.

Wasu sun kira hakan a matsayin barnatar da kudin talakawan kasar masu biyan haraji yayin da wasu kuma ke sukar gazawar gwamnatin na inganta harkokin kiwon lafiyar da suka tabarbare.