✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Press To Play

An yi Sallar Jana’izar mutum 15 da gobarar New York ta kashe

An gudanar da jana’izar mutum 15 da suka rasu a wata gobara da ta tashi a gundumar Bronx da ke birnin New York a makon…

An gudanar da jana’izar mutum 15 da suka rasu a wata gobara da ta tashi a gundumar Bronx da ke birnin New York a makon da ya gabata, wadda ta hallaka mutum 17 ciki har da kananan yara takwas.

Gwamnatin Jihar New York ta ware Dala miliyan biyu ta kafa gidauniyar bayar da diyya ga wadanda wannan balai’i ya rutsa da su.

Mataimakin Gwamnan jihar, Brian Benjamin, ya samu halartar jana’izar tare da Magajin Garin, New York, Eric Adams da Shugaban Masu Rinjayi a Majalisar Dattawar Amurka, Chuck Schummer.

Daruruwan mutane daga sassa daban-daban na gudumar Bronx da ma New York baki daya, musamman Musulmi ne suka halarci Sallar Jana’izar ta mutum 15 a ranar Lahadi a cikin yanayi mai tsananin sanyi.

Wasu mata da suka halarci jana’izar

Muryar Amurka ta ruwaito cewa, mutanen da suka halarci jana’izar sun bayyana matukar bakin ciki da alhini na rashin ’yan uwansu ’yan Afirka wadanda kusan dukkansu ’yan kasar Gambiya ne.

Antoni-Janar na New York, Leticia James, ta lashi takobi cewa hukumarta za ta yi iya bakin kokarinta ta tabbatar da an gurfanar da duk wani mai laifi a wannan gobara da ta tashi, wanda jami’ai suka ce injin dumama gida da wata kofar da ta lalace aka bar ta a sake ne suka haddasa gobarar.

Yadda aka gudanar da jana’izar mamatan

Mataimakin Gwamnan Jihar New York, Brian Benjamin, da ya wakilici gwamnar, ya ce, “Muna tabbatar wa iyalai da suke nan da ma waje cewa Bronx na cikin Jihar New York kuma za mu kasance tare mu tabbatar wannan bala’i bai sake faruwa ba.

“Shi ma Shugaban Majalisar Dattawa, Chuck Shummer, zai yi duk iya kokarinsa a matsayi na tarayya a taimaka wa iyalai,” inda ya ce sun bukaci Ofishin Jakadancin Amurka a Gambiya da ya daina aiki saboda annobar COVID-19.