✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An yi raba daidai tsakanin maza da mata a sabuwar gwamnatin Jamus

Gwamnatin za ta kunshi maza 8, mata 8, sai jagoranta namiji.

Sabuwar gwamnatin da za a kafa a kasar Jamus, karkashin jagorancin Olaf Scholz, wanda zai gaji Angela Merkel, a matsayin sabon Shugan gwamnati, a ranar Litinin ta ayyana sunan sabbin ministoci 17 din da za ta nada.

Daga cikin kunshin Ministocin dai, takwas za su kasance mata ne, maza kuma tara.

Gwamnatin dai za ta kasance ta hadin gwiwa ce tsakanin manyan jam’iyyun SPD da FDP da kuma Greens.

Jam’iyyar SPD mai rinjaye dai ta tura da sunan maza hudu da mata uku, sai takwararta ta FDP da ta tura maza uku da mace daya, yayin da jam’iyyar Greens ta bayar da mata uku da maza biyu.

Hakan dai na nufin gwamnatin za ta kunshi maza takwas da mata takwas, yayin da Olaf Scholz zai kasance jagoran gwamnatin.

Tun ma kafin zaben da aka gudanar a watan Satumba, Shugaban SPD ya ce zai yi kokarin kawo daidaito tsakanin adadin maza da mata a kunshin gwamnatin.

“Gwamnatin da za ta kasance karkashina, za ta kasance akalla rabinta mata ne,” kamar yadda Olaf Scholz ya taba wallafa wa a shafinsa na Twitter a shekarun baya. (NAN)