Hukumar kashe gobara ta Najeriya (FFS) ta yi nasarar kashe gobarar da ta tashi a ofishin Akanta-Janar na Najeriya, AGF, Ahmed Idris, da safiyar ranar Laraba.
Jami’in hulda da jama’a na Hukumar FFS ne ya sanar da hakan a shafinsa na Facebook, inda maida martani game da hotunan da ake yada wa lokacin da gobarar ke ci, ya ce jami’an su sun yi nasarar kashe gobarar da ta kama ginin ofishin.
Da safiyar ranar Laraba ne gobarar ta tashi a ofishin Akanta-Janar, ba a samu rahoton asarar rai ba lokacin da gobarar ta tashi.
Wasu daga cikin ofisoshi a birnin tarayya Abuja na ci gaba da gudanar da ayyukansu duk da dokar hana fita da Shugaba Muhammadu Buhari, ya bada umarni don kaucewa yaduwar annobar cutar coronavirus a birnin.
Sai dai wasu masu sharhi na zargin cewa, an dai bankawa ofishin wuta ne da gan-gan bayan jam’iyyar adawa ta PDP ta bukaci gwamanti mai ci ta yi mata bayanin yadda aka kashe kudin tallafi da ya kai Naira tiriliyan 2.
Mataimaki na musamman ga tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, Reno Omokri ya ce za a binciki musabbabin tashin gobarar.
The fire in the Accountant General’s office started a day after @OfficialPDPNig called for an audit into the so called subsidy regime that General @MBuhari’s government claims to have spent over ₦2 trillion on? How convenient! Who is fooling who? #FreeLeahSharibu #RenosNuggets
— Reno Omokri (@renoomokri) April 8, 2020