✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi musayar wuta da ’yan bindiga a kusa da filin jirgin saman Kaduna

Lamarin dai ya tilasta rufe filin na dan wani lokaci

Rahotanni na cewa an yi musayar wuta tsakanin sojoji da wasu ’yan bindiga a kusa da filin jirgin saman kasa da kasa da ke Kaduna ranar Asabar.

Lamarin, wanda ya faru wajen misalin karfe 12:30 na rana, a cewar wasu ganau, ya tilasta rufe filin jirgin na dan wani lokaci.

Aminiya ta gano cewa wani jirgin sama na kamfanin AZMAN na dab da tashi daga filin don tafiya Legas, lokacin da lamarin ya faru.

Wata majiya a cikin filin ta ce babu jirgin da aka kai wata hari.

A cewar majiyar, tilas kasancewar ’yan bindigar kusa da filin jirgin ta sa aka dakatar da tashinsa.

Daga bisani dai an ce an girke jami’an sojoji a filin don dawo da doka da oda.

Duk yunkurin wakilinmu na jin ta bakin kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, ya ci tura har zuwa lokacin hada wannan rahoton.