✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi wa ma’aikatan ƙananan hukumomin Gombe ƙarin albashin N5,000

Gwamnatin Jihar Gombe ta amince da biyan ƙarin albashin Naira 5,000 ga ma’aikatan ƙananan hukumomi

Gwamnatin Jihar Gombe ta amince da biyan ƙarin albashin Naira 5,000 ga ma’aikatan ƙananan hukumomi da Hukumar Ilimi ta Ƙananan Hukumomi (LGEA).

Ƙarin albashin zai fara aiki ne daga albashin watan Yuni na shekarar 2025

Wata sanarwa da Jibrin Yusuf ya sanya wa hannu a madadin Shugaban Ma’aikatan Gwamnati, Ahmed Abdullahi, ta ce cimma matsayar ne a wani taro na musamman da aka gudanar a ranar Talata.

Taron ya samu halartar Shugaban Ma’aikata tare da wakilan ƙungiyoyin kwadago da wasu manyan jami’an gwamnati.

Ta ce an amince da ƙatin Naira 5,000 ga ma’aikatan har sai an kammala aikin tantancewa da ake gudanarwa a halin yanzu.

Shugaban Ma’aikata ya umarci Ma’aikatar Kuɗi daCi-gaban Tattalin Arziki da ta gaggauta ɗaukar matakan da suka dace don ganin an aiwatar da wannan karin cikin lokaci.

Duk da wannan ƙarin, binciken da wakilinmu ya gudanar ya gano cewa har yanzu ma’aikatan ƙananan hukumomi 11 na jihar ba su fara cin gajiyar ƙarin albashi da aka yi ba.

Mataimakin Gwamnan Jihar, Dokta Manassah Jatau, tare da shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago (NLC) reshen jihar, Yusuf Bello, sun amince cewa idan kuɗaɗen shiga sun ƙaru, za a fara biyan mafi karancin albashi na Naira dubu 70,000 ga ma’aikata.

A yayin bikin Ranar Ma’aikata da aka gudanar kwanan nan, Yusuf Bello ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta fara aiwatar da biyan mafi karancin albashi ga ma’aikatan kananan hukumomi cikin gaggawa.