A daidai lokacin da take fama da hauhawar farashin kayayyaki da kuma karyewar kudin kasarta, Turkiyya ta sanar da yi wa ma’aikatanta karin albashi da kaso 50 cikin 100.
Shugaban Kasar, Recep Tayyip Erdogan, wanda ya sanar da hakan yayin wani taron manema labarai da aka watsa ta kafafen yada labaran kasar ranar Alhamis ya ce karin shi ne irinsa mafi girma a tarihin kasar cikin shekara 50.
- Indiya za ta kara mafi karancin shekarun aurar da mata daga 18 zuwa 21
- Babu shugaban da zai iya kawar da ’yan bindiga a 2023 —Lai Mohammed
Karin dai na nufin yanzu mafi karancin albashi a kasar zai kai kudin kasar na Lira 4,250, kwatankwacin Naira 137,500, sabanin Lira 2,826 (N91,000) da ake biya a baya.
Bugu da kari, karin albashin zai shafi kimanin ma’aikata miliyan shida a kasar.
Erdogan ya ce, “Mun himmatu wajen rage wa mutane halin rashin tabbas din da suka fada sakamakon tashin gwauron zabon da kayayyaki suka yi, da kuma ci gaba da karyewar darajar kudin kasarmu.”
Shugaban ya kuma sanar da cewa kasar za ta dauke wa ’yan kasar biyan wasu kudaden haraji daga cikin sabon albashin.
Tattalin arzikin kasar Turkiyya dai na shan fama da kalubale, ta inda sai da darajar kudin kasar ta ragu da kusan rabi, in aka kwatanta ta da Dalar Amurka tun farkon watan Janairun bana.
Alkaluman hauhawar farashin dai ya haura kaso 21 cikin 100 wanda Babban Bankin Kasar ya yi harsashe.
Sai dai jam’iyyun adawa a kasar na harsashen ta yiwu alkaluman ma sun wuce haka.