✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Batar N4bn: An maka Shugabannin Majalisun Tarayya a kotu

Kungiyar SERAP mai fafutikar kare hakkin bil’adama da ci gaba tattalin arziki, ta yi karar Shugabannin Majalisun Tarayyar Najeriya a gaban Babbar Kotun Tarayya, bisa…

Kungiyar SERAP mai fafutikar kare hakkin bil’adama da ci gaba tattalin arziki, ta yi karar Shugabannin Majalisun Tarayyar Najeriya a gaban Babbar Kotun Tarayya, bisa zargin sun gaza binciko batan Naira biliyan 4.4 na kasafin Majalisar.

SERAP ta nemi Kotun ta dauki hukunta Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan da na Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila, yayin da suka aiwatar da duk wata mai yiwuwa a kan batan kudin.

Kungiyar tana kuma neman kotun da ta tursasa su mika matsalar gaban hukumomin yaki da cin hanci a yayin da Ofishin Babban Mai Binciken kudi na kasar ya nuna damuwa a kan zargin sace kudaden.

Masu karar na bukatar a tilasta wa Shugabannin Majalisar da su yi amfani da karfin ikon da kundin tsari mulki ya tanada wajen gudanar da bincike a fili da zai gamsar da kowa kan batan kudaden.

“Gazawar Majalisun na gudanar da bincike da kuma rashin mika wa hukumomin da ke bincike kan cin hanci bayanai a 2015 da 2017 da 2018 ya saba wa manufar da aka kafa ofisoshinsu a kai.

“Haka kuma yana cin karo da sashe na 4 da na 88 da kuma na 89 na kundin tsarin mulkin kasar,” a cewar sanarwar da SERAP ta fitar.

Ana iya tuna cewa, SERAP a wasikar da ta aike a ranar 30 ga Janairun 2021, ta bukaci Shugabannin Majalisun da su hanzarta amfani da karfin ikonsu wajen binciko yadda aka batar da Naira biliyan 4.4 na kasafin kudin Majalisun da suke jagoranta.