An sallaci gawar Sarkin Gaya, Alhaji Ibrahim Abdulkadir, tare da kai shi makwancinsa.
An yi jana’izar gawar Sarkin Gaya ne da yamma a Kofar Fadar garin Gaya, bayan ya rasu a safiyar ranar Laraba 22 ga watan Satumba, 2021.
- Shehun Borno ya amince tsoffin ’yan Boko Haram su dawo cikin al’umma
- Sarkin Gaya, Alhaji Ibrahim Abdulkadir, ya rasu
Sarki Ibrahim ya bar duniya yana da shekara 91 bayan fama da rashin lafiya.
Rasuwarsa ta zo ne shekara biyu bayan zamansa Sarkin Gaya a shekarar 2019.
Buhari ya yi alhinin rasuwar Sarkin Gaya
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana jimaminsa game da rayuwa Sarkin Gaya, Alhaji Ibrahim Abdulkadir.
A sakon Buhari na ta’aziyyar rasuwar Sarkin Gaya, mai magana da yawunsa, Garba Shehu, ya fitar, ya bayyana mamacin da cewa “yana daga cikin sarakunan kasar nan da suka kare mutucin sarautun gargajiya.”
Mutumin kirki ne da ya hidimta wa al’ummarsa da sadaukar da kai kuma za a jima ana tunawa da shi da hakan.
Ya kuma jajanta wa Masarautar Gaya al’ummar masarautar da kuma Gwamnatin Jihar Kano game da rasuwar tare da addu’ar Allah Ya gafarta masa Ya kuma rahamshe shi.