✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi jana’izar dan sandan da aka kashe a Jihar Ribas

A ranar Litinin da ta gabata ne aka yi jana’izar dan sandan nan da aka yi wa kisan gilla yayin gudanar da zaben cike- gurbi…

A ranar Litinin da ta gabata ne aka yi jana’izar dan sandan nan da aka yi wa kisan gilla yayin gudanar da zaben cike- gurbi a Jihar Ribas a ranar Asabar da ta gabata.

dan sannda Sufurtanda Muhammad Alkali, mahaifinsa, wanda tsohon Kwamishinan ’Yan sanda Alhaji Yakubu Alkali da Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Neja Alhaji Zubairu Mu’azu ne suka tarbi gawarsa lokacin da ta iso garin Minna da misalin karfe daya da rabi na ranar.
An yi jana’izarsa ne a garinsu da ke karamar Hukumar Bosso a Jihar Neja.