An gudanar da jana’izar tsohon Ministan Harkokin Cikin Gida na Najeriya kuma Sardaunan Dutse, Alhaji Bello Maitama Yusuf, a Fadar Sarkin Kano da yammacin Juma’a.
Marigayin dai ya rasu ne yana da shekara 76 a duniya, bayan gajeruwar jinya.
Ya rasu ya bar mata biyu da ƴaƴa 10; maza biyar, mata biyar.
Marigayin dai ƙwararran lauya ne wanda ya yi Minista a jamhuriya ta biyu kuma ya zama Sanata a jamhuriya ta huɗu.
An birne shi ne a makabatar Tarauni da ke birnin Kano kamar yadda Addinin Musulunci ya tanadar.
Ga wasu daga cikin hotunan jana’izar tasa: