✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka daura auren ‘zawarawa’ 1,800 a Kano

An daura auren ne a Kananan Hukumomin jihar 44

Gwamnatin Jihar Kano a ranar Juma’a ta gudanar da daurin auren zawarawa da ’yan mata 1,800 wanda ta dauki watanni tana shiryawa.

Aminiya ta rawaito cewa sabanin a baya da ake daura auren a waje guda, a wannan karon an daura shi ne a dukkan Kananan Hukumomin Jihar guda 44.

Sama da aure 300 dai aka daura a Karamar Hukumar Birni da Kewaye, wanda ya gudana a Babban Masallachin Birnin Kano bayan Sallar Jumaa.

Jagoran darikar Kwankwasiyya, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ne ya zama waliyyin amare, yayin da Gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya zama waliyyin angwaye inda ya biya sadakin kowacce amarya akan Naira dubu 50.

A jawabinsa a yayin bikin, Sanata Kwankwaso ya yi godiya ga Allah da ya nuna musu ranar, wacce ya ce tana da matukar muhimmanci a gare su duba da yadda dimbin al’umma suka karbi shirin na gata.

Ya kuma yi fatan alheri ga ma’auratan tare da addu’ar samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Wani ango mai suna Ahmad Ali da Aminiya ta zanta da shi ya bayyana farin cikinsu game da samun shiga cikin auren, inda kuma ya yi addu’ar fatan alheri ga Gwamnatin Kano saboda kirkiro da shirin.