Babbar Kotun Jihar Kano ta halasta wa ’yan kasuwar Sabon Gari shagunan da ke bangaren ’yan barkono da gidajen wanka.
Kotun ta kuma umarci hukumar gudanarwar kasuwar Sabon Gari da Shugabanta su biya diyyar N200,000 ga ’yan kasuwar saboda bata musu lokaci.
Tunda farko masu karar, Alhaji Musa Yakubu da wasu mutane 7 sun je gaban kotun ne suna karar hukumar gudanarwar Kasuwar Muhammadu Abubakar Rimi wato Sabon Gari da shugaban hukumar.
Masu karar sun nemi kotun ta tabbatar da yarjejeniyar da ke tsakanin ’yan kasuwar da hukumar kasuwar.
Sun bayyana wa kotun cewar tun zamanin mulkin soja suka kulla yarjejeniya da hukumar kasuwar a kan za su gina shaguna a filin kasuwar kuma za su sabunta biyan haraji bayan shekaru 15, amma kafin shekaru 15 din su cika hukumar kasuwa ta karbe shagunan.
Da take sanar da hukuncin, Mai sharia Dije Aboki. ta bayyana cewar wannan yarjejeniya da ke tsakanin kungiyar ’yan kasuwar da hukumar kasuwar halastacciya ce kuma kotun ta tabbatar da ita.
Mai Shari’a Dije Aboki ta kuma halastawa ’yan kasuwar ta sabon gari bangaren barkono da gidajen wanka shagunan da suka mallaka a karkaahin waccan yarjejeniya.
Kotun ta kuma bayyana cewar hukumar gudanarwar kasuwar Sabon Gari da Shugaban Hukumar Hisbah za su biya Naira dubu dari biyu ga ’yan kasuwar na bata musu lokaci da suka yi.