✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An yi gwanjon kwallon da Maradona ya ci da hannu kan $2m

Kafin yanzu aka kiyasta cewa farashinta zai kai fam miliyan 3.

An yi gwanjon kwallon da tsohon dan kwallon Argentina, Marigayi Diego Maradona ya jefa raga da hannu a shekarar 1986 a kan dala miliyan 2.3.

Tun a watan Oktoban da ya gabata aka sanya gwanjon kwallon wadda marigayin ya jefa a wasan daf da na kusa da karshe na Gasar Cin Kofin Duniya a shekarar 1986 tsakanin Ingila da Argentina.

An sayar da kwallon ce a ranar 16 ga watan Nuwamba a matsayin wani shiri na musamman na Gasar Kofin Duniya ta bana da za a yi a Qatar.

Kwallon dai na daya daga cikin kwallayen da suka fi shahara a tarihi a tamaula, wadda kafin yanzu aka kiyasta cewa farashinta zai kai fam miliyan 3.

Ali Bin Nasser dan kasar Tunisia, shi ne alkalin da ya busa wasan da ya bayar da kwallon da Maradona ya ci wadda ake kira Hand of God a wasan.

Bin Nasser ya ce: “Wannan kwallon na cikin tarihin kwallon kafa – wannan ne daidai lokacin da ya dace a nuna wa duniya ita.”

An yi amfani da kwallon na tsawon minti 90 na wasan, wadda ita ce kwallon da aka fi bayyanawa a matsayin mai cike da rudani idan ana maganar tarihin Kofin Duniya.

Maradona ne ya fara cin kwallo a wasan – ta hanyar naushinta kuma kwallon ta wuce mai tsaron ragar Ingila, Peter Shilton.

Bin Nasser bai duba kwallon ba ya bayar da ita, yayin da dan wasan daga baya ya yi bayanin cewa “rabin kwallon ya taba kan dan wasan rabi kuma kan Maradona.”

Kwallo ta biyu da ya ci a wasan ta yi sunan da ake kiranta da “kwallon karni”, inda ya yanka mutum biyar daga cikin ’yan wasan Ingila sannan ya yanka Shilton ya ci.

Argentina ce ta yi nasara a wasan da ci 2-1 kuma daga karshe ta ci Kofin Duniyar da aka yi a Mexico.

Idan ba a manta ba, a watan Mayun da ya gabata ne aka yi gwanjon rigar da Maradona ya sanya a wasan a kan dalar Amurka miliyan 9.3, fiye da ninki biyu na darajarta da aka yi hasashe.

Ana sa ran za a gabatar da rigar a yayin Gasar Kofin Duniya ta bana da za a soma a mako mai zuwa.