✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An yi gwanjon kujerar tafiya duniyar wata kan Naira biliyan 11.5

Za a yi balaguron zuwa duniyar watan a ranar 20 ga watan Yuli.

Kamfanin Blue Origin na attajirin Ba’amurken nan mai suna Jeff Bezos, ya sayar da wajen zaman mutum guda a cikin kumbon New Shepard da zai je duniyar wata ranar 20 ga watan Yuli kan Dala miliyan 28, kwatankwacin Naira biliyan 11.5 a kudin Najeriya.

Mutum 20 da suka shiga gasar sayan wajen zaman bayan da kamfanin ya kada kararrawar yin gwanjon kujerar, sun fara saka tayin Dala miliyan 4.8 a cikin minti 10 da aka yi ana gwanjon, amma a minti ukun karshe gasar neman kujerar ta hauhawa.

Da farko dai kimanin mutum 7,600 da suka fito daga kasashe 159 suka nuna sha’awar shiga gasar kamar yadda kamfanin ya sanar a karshen mako.

Wanda ya samu nasarar sayan kujerar da yanzu ba a bayyana ko wane ne ba, zai shiga sahun mutumin da ya kafa kamfanin na Amazon, Jeff Bezos da kaninsa, Mark a bulaguron zuwa duniyar watan.

Shawagin da kumbon da ke sarrafa kansa wanda zai shafe minti 11, shi ne na 16 amma na farko da ke dauke da dan Adam zuwa duniyar watan – zai tashi daga yankin Van Horn a Jihar Texas.

A makon jiya, attajiri Bezos, wanda zai sauka daga shugabancin kamfanin Amazon ana saura kwana 15 gabanin bulaguron, ya wallafa a shafinsa na Instagram: “Tun ina dan shekara biyar nake mafarkin tafiya zuwa duniyar wata.

“A ranar 20 ga watan Yuli, zan yi wannan bulaguron tare da kanina wanda shi ne jigon tafiyar tare da babban abokina.”

Tafiyar da attajirin zai yi na zuwa ne a daidai lokacin da ake ganiyar gogayyar zuwa duniyar watan tsakanin manyan attajiran duniya.

Bezos, wanda ya kashe kimanin Dala biliyan daya cikin shekara guda daga ribar da kamfaninsa domin aikin kumbon na Blue Origin, ya kwatanta bulaguron da za su yi a zaman matuka jirgin sama a farkon shekarun kirkirar jiragen sama a duniya.

Kamfanin ya kuma ce kudin gwanjon kujerar za a kai su asusun gidauniyar kumbon na Blue Origin, domin zuriyar da ta zo nan gaba da zimmar ba ta karsashin bidar ilimin kimiyya da fasaha da injiniyanci da kuma lissafi, wanda a Turance ake kira STEM a takaice.

%d bloggers like this: