An sayar da rigar da Buzz Aldrin, wani dan sama jannati ya je Duniyar Wata da ita a kan Dala miliyan biyu da dubu 700, kwatankwacin sama da Naira biliyan daya a cinikin gwanjo.
An sayar da rigar ce a birnin New York ta Amurka, a ranar Talata, inda aka sayar da ita ga wanda ya yi tayi ma fi tsoka.
- Matsalar tsaro: Sanatoci sun yi barazanar tsige Buhari
- Dan Sanda ya yi wa ’yar dan uwansa fyade ta yi ciki
Rigar, wacce fara ce, na dauke da tutar Amurka a gabanta, da kuma tambarin Hukumar Binciken Sararin Samaniya ta Kasar (NASA) mai kula da hatrkokin sararin samaniya ta kasar, da ita Buzz ya je duniyar wata a jirgin kumbo Appolo 11.
Rigar mai matukar tarihi na daya daga cikin abubuwan da dan sama jannatin Buzz mai shekara 90 da haihuwa, ya yanke shawarar ya sayar a yanzu, bayan damunsa da tayi da aka yi ta yi.
Buzz Aldrin ya sa rigar ce a lokacin da suka hau kumbo Appolo 11, suka kuma sauka a duniyar wata a shekarun 1960.
“Mutane da yawa sun dade suke bibiyata da in sayar musu da wannan riga, ban yi haka ba, sai yanzu,” inji Buzz.
Aldrin shi ne kadai ya ke raye a cikin mutane ukun da suka je Duniyar Wata, a cikin jirgin kumbo Appolo 11, wanda suka kafa tarihi a duniya.