✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi girgizar kasa sau 2 a rana daya a kasar China

An samu girgizar kasa har sau biyu a kasar China cikin kasa da kwana guda abin da kawo yanzu ya yi sanadiyar mutuwar mutane 7…

An samu girgizar kasa har sau biyu a kasar China cikin kasa da kwana guda abin da kawo yanzu ya yi sanadiyar mutuwar mutane 7 da jikkatar wasu sama da 60 a larduna Dinjian da Sichuan kamar yadda BBC ta ruwaito.

Girgizar baya-bayan nan ta faru ne a kusa da kan iyakar kasar ta China da kasar Kazakhstan, a lardin Dinjian.

Amma kuma ta farkon wadda ta afka wa wani yanki mai tsaunuka da ke Kudu maso yammacin kasar ta hallaka akalla mutane 7, tare da jikkata wasu da dama.

Girgizar ta kuma faru ne a kusa da wani sanannen wurin zuwan baki ‘yan yawon bude ido da ke lardin Sichuan da ake kira da gandun dajin Jiuz-haigou.

Sannan kuma an samu zafrewar laka, wadda ta rutsa da ‘yan yawon bude ido kusan dari, tare da lalata dubban gidaje.

Inda girgizar da ta fi mun ta faru ne a wani yanki ne da ke da karancin jama’a da galibi ‘yan kabilar Tibet ne ke zaune.

Wasu rahotanni sun ce adadin wadanda suka mutun zai iya karuwa.

Lardin Sichuan yanki ne da ke fuskantar barazanar yawan afkuwar girgizar kasa.

Mutane fiye da 70,000 suka mutu a girgizar kasar a shekara ta 2008.

Wasu hotuna sun nuna lalatattun gine-gine, da suka hada da otal a garin Jiuzhaigou, inda ke da sanannen wurin adana kayan tarihi na duniya da Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana.

Wata mai gidan abinci a garin ta ce karfin girgizar kasar ya fi na shekara ta 2008, duk da cewa babu wasu bayanai da suka nuna cewa adadin wadanda suka mutu zai kai ko kusa da wanda ya faru a wancan lokacin.

Tang Sesheng ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, mutane da dama sun tsere daga gidajensu a garin na Jiuzhaigou.

“Mutane ba su iya saukar komai ba kama daga kudi ko tufafi ba, mun kawai ruga da gudu ne,’’ inji ta.