✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An yi garkuwa da wata mata bayan sa’a 24 da mutuwar mijinta a Katsina

A ranar Talata ce mijin matar ya rasu.

’Yan bindiga sun yi garkuwa da matar tsohon Dagacin Kauyen Kofa na Karamar Hukumar Kusada da ke Jihar Katsina, Alhaji Rabe Bello Kofa.

Wani mazaunin garin da ya bukaci a sakaya sunansa ya shaida wa Aminiya cewa maharan sun far wa kauyen ne da sanyin safiyar Laraba.

Mazaunin ya ce kai tsaye maharan suka nufi gidan Dagacin Kauyen da ya rasu ranar Talata, inda suka yi awon gaba da wasu iyalansa da ke zaman makoki ciki har da matarsa.

“Maharan sun kutsa gidan marigayin inda suka yi awon gaba da wasu iyalansa biyar ciki har da mai dakinsa, amma daga bisani sun saki sauran hudun suka yi garkuwa da matar,” in ji shi.

A ranar Talata ce Dagacin Kofa wanda dan uwan tsohon Kakakin Majalisar Katsina ne ya rasu kuma a wannan rana ce aka yi jana’izarsa kamar yadda majiyar ta bayyana.

Da aka nemi jin ta bakin Kakakin ’yan sandan Katsina, SP Gambo Isah ya ce zai tuntubi jami’in da ke kula da yakin.

%d bloggers like this: