✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An yi garkuwa da wani dan kasuwa a Jalingo

Maharan sun sace dan kasuwar ba tare da kowa ya sani ba.

Wasu ’yan bindiga a garin Jalingo na Jihar Taraba sun yi garkuwa da wani fitaccen dan kasuwa, Abdu Yarima a daren Lahadi.

Dan kasuwar, wanda ke sana’ar sayar da babura masu kafa uku (Keke Napep), an yi garkuwa da shi ne da misalin karfe 11:30 na daren ranar Lahadin a gidansa da ke Kasuwan Yelwa a birnin na Jalingo.

Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa, maharan wanda adadinsu ya kai tara, sun shiga gidan dan kasuwar kai tsaye sannan suka sace shi.

Sai dai ba su yi harbi ko daya ba yayin da suka shiga gidan, inda suka wuce har cikin dakinsa sannan suka tafi da shi ba tare da makwabtansa sun sani ba.

Rahotanni sun ce sai bayan sace dan kasuwar da wasu lokuta sannan iyalansa suka sanar da mutane abin da ya faru.

Kakakin ’yan sandan Jihar, DSP Usman Abdullahi bai amsa wayar wakilinmu ba don jin ta bakinsa game da faruwar lamarin.