✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An yi garkuwa da mutum 50 a Neja

’Yan bindiga a kan babura sun yi awon gaba da mutum 50 a garin Bassa.

Akalla mutum 50 ne aka yi garkuwa da su a Karamar Hukumar Shiroro ta Jihar Neja, bayan harin da ’yan bindiga suka kai a garin Bassa.

’Yan bindiga a kan babura sun kai wa garin hari ne da sanyin safiya a yayin da mutane ke shirin fara harkokinsu, wanda hakan ya sa mazauna tserewa zuwa cikin dazuka.

Da yake tabbatar da harin, Shugaban Kungiyar Matasa Masu Kishin Shiroro, Sani Abubakar Kokki ya bayyana maharan a mtsayin ’yan ta’adda masu tayar da zaune tsaye da hana al’umma zama cikin kwanciyar hankali.

Sai dai a lokacin ya ce babu tabbaci game da ainihin adadin mutanen da aka yi garkuwa da su, amma ya tabbatar cewa suna da yawa.

Sani ya ce ko a ranar Talata, sai da aka kai wa wasu al’ummomi hari a yankin Bassa/Kokki inda aka kashe mutane da dama.

Shugaban Matasan ya ce ce Karamar Hukumar Shiroro na matukar bukatar dauki domin kawo karshen ayyukan miyagun da ke salwantar da rayuka ba gaira, ba dalili.

Aminiya ta tuntubi kakarin ’yan sanda a Jihar Neja, ASP Abiodun Wasiu, ama ya ce zai waiwaye ta idan ya samu cikakken bayani.