’Yan bindigar da suka yi garkuwa da fitaccen mai gidan rawar nan da aka fi sani da ‘Club 64’ na birnin Yenagoa a Jihar Bayelsa, Tari Ajanami, sun sake sace wadanda suka je domin biyan kudin fansarsa.
Masu garkuwar dai sun saki mai gidan rawar, amma sun yi awon gaba da matarsa mai kimanin shekara 38 a duniya, Christiana da kuma mahaifinta mai shekara 74.
- COVID-19: Saudiyya za ta biya iyalan ma’aikatan lafiyar da suka mutu N54m
- Najeriya ta kammala gasar Olympics a mataki na 74
Sun dai bukaci a biya su Naira miliyan 20 ne a matsayin kudin fansa amma suka sami miliyan 15.
An dai sace Tari Ajanami ne a watan da ya gabata a gidansa da ke kan hanyar Otioti na birnin Yenagoa, kafin daga bisani a sake shi a Karamar Hukumar Ahaoda ta Jihar Ribas ranar Alhamis.
Aminiya ta gano cewa an biya kudin fansar ne cikin sirri kamar yadda masu garkuwar suka bukata.
Wani dan uwan wadanda aka sace din da bai amince a ambaci sunansa ba ya ce babbar fargabarsu ita ce matar tana fama da cutar awan Jini, kuma ba ta tare da magungunan da take sha lokacin da suka kama ta.
“Muna rokonsu da su ji tausayinta,” inji shi.
Da wakilinmu ya tuntubi kakakin ’yan sanda na Jihar, SP Asinim Butswat, ya ce har yanzu rundunar ba ta sami rahoton sace mutanen ba.
Gabanin sace mai gidan rawar dai, an yi garkuwa da mahaifiyar Sakataren Gwamnatin Jihar ta Bayelsa mai kimanin shekara 80, Uwar-Gida Betinah Benson a birnin na Yenagoa.
Sai dai har yanzu babu tabbacin ko an sako mahaifiyar dan siyasar ko kuma a’a.