✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi garkuwa da mutum 12 a gidan Sarkin Kagarko

’Yan bindiga sun afka gidan Sarkin Kagarko da ke Karamar Hukumar Kagarko ta Jihar Kaduna, Alhaji Sa’adu Abubakar, inda su ka yi awon gaba da…

’Yan bindiga sun afka gidan Sarkin Kagarko da ke Karamar Hukumar Kagarko ta Jihar Kaduna, Alhaji Sa’adu Abubakar, inda su ka yi awon gaba da amaryarsa da wasu kananan yara da jikoki tara.

Maharan sun kutsa gidan Sarkin ne Ranar Lahadi da misalin karfe 11:15 na dare, suka yi kokarin tafiya da shi, amma ya shaida musu cewa ba zai iya ba, saboda ba shi da lafiya.

Sai suka bukaci ya ba su kudi, amma da ya shaida musu ba shi da komai nan take suka yi awon gaba da kananan yara da suka hada da jikokinsa mutum tara tare da amaryarsa kafin su fita zuwa wani gidan.

Majiyar Aminiya daga garin Kagarko da ta bukaci a sakaya sunanta ta shaida wa wakilinmu cewa amaryar Sarkin ta samu kubuta daga ’yan bindigan, amma dai sun yi tafi da wata budurwa da wani yaro sai wani bako da yazo daga jihar Kano.

“A kan hanyarsu ta guduwa sun shiga gidan dan uwana mai suna Audu Kwakulu da ke Unguwan Pah inda suka harbe shi a gefen ido; a yanzu haka yana asibiti a nan garin Kagarko,”  in ji shi.

Ya ce mutumin da aka harba ya fito kawo dauki ne bayan ya ji ihun wata mata da ke kururuwan neman dauki, inda suka harbe shi a gefen idonsa.

Majiyar ta Aminiya ta ce ’yan bindigar sun yi ta harbe-harben a garin tare da farfasa tagogin gidaje.

Lokacin da wakilinmu ya tuntubi kakakin rundunar ’yan Sandan jihar Kaduna, DSP Muhammed Jalige ta wayar tarho bai amsa ba, har aka kammala hada wannan rahoton.