✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi garkuwa da matar Mataimakin Akanta-Janar na Katsina

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da matar Mataimakin Akanta- Janar na jihar Katsina Hajiya Lubabatu Sani Lawal BK bayan sun shiga cikin gidanta. Majiyarmu…

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da matar Mataimakin Akanta- Janar na jihar Katsina Hajiya Lubabatu Sani Lawal BK bayan sun shiga cikin gidanta.

Majiyarmu ta samu rahotan cewa, ‘yan bindigar da suka su kimanin goma sun shiga cikin gidan Hajiya Lubabatu, ne da yake unguwar rukunin gidajen gwamnati da misalin karfe 9 na dare ranar Laraba.

Rahotan na bayyana cewa, ‘yan bindigar sun shiga gidan da kananan motoci biyu daya kirar 206, sannan suka fara dukan wasu da ke cikin gidan sannan suka binciko inda take suka sace.

Har zuwa yanzu masu garkuwan ba su kira ba don neman kudin fansa kafin a sako Hajiya Lubabatu.