✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An yi garkuwa da malamin Jami’ar ABU

An yi garkuwa da malamin a cikin jami'ar kwana biyu bayan dalibai tara sun kubuta

A daren Lahadi ne wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane suka kutsa cikin Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya suka yi awon gaba da wani malami da iyalansa.

Malamin mai suma Dokta Ibrahim Bako da ke Tsangayar koyar da aikin likitanci ya fada tarkon masu garkuwar ne kwanaki biyu bayan wasu daliban jami’ar tara sun kubuta.

Jami’in Hulda da Jama’a na jami’ar, Malam Auwal Umar ya shaida wa Aminiya cewa maharan sun kutsa rukunin gidajen ma’aikatan jami’ar da ke ‘Area BZ’ cikin dare suka yi awon gaba da malamin da matarsa daga bisani suka jefar da matar da diyarsa a kauyen Da’a da ke Karamu Karau.

Malam Auwal ya ce tuni sashen tsaro na jami’ar tare da hukumomin tsaro suka fara bin sawun lamari.

%d bloggers like this: